Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran kasar Lebanon sun rawaito cewa an kai hari kan wani babur a kan hanyar Ain Baal-Aitit a birnin Tyre na kasar Lebanon.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, wani dan kasar Lebanon ya yi shahada sakamakon harin da jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a garin Ain Baal da ke kudancin kasar Lebanon.
Wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa an kai hari kan wannnan babur din a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan Ain Baal da Al-Bazouria a harin.
Ita tashar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton shahadar wani dan kasar Lebanon a harin.
A ranar Talata 9 ga watan Satumba ma gwamnatin mamaya na yahudawan sahyoniya da ke ci gaba da kai hare-hare a kudancin kasar Lebanon, sun kai hari kan wata mota da wani jirgin sama mara matuki a yankin Al-Kharroub da ke kudancin birnin Beirut.
An kai harin ne a kusa da birnin Al-Jiya mai tazarar kilomita 30 daga babban birnin kasar. Jirgin da aka kai harin da shi ya nufi motar ne daga kusa da masallacin da ke unguwar "Zarot" da ke tsakanin garuruwan Al-Jiya da Barja a yankin Al-Kharroub.
Wannan harin dai ya faru ne kwana guda kacal bayan wasu jerin hare-hare da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke kai a gabashin kasar Lebanon, wanda a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar, ya yi sanadin shahadar 'yan kasar Lebanon biyar.
Your Comment